Daga ranar 16 zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Kazakhstan da Uzbekistan da Kyrgyzstan, inda ya ziyarci jami’ar Al-Farabi, da jami’ar Ablai Khan dake nazarin alaƙar ƙasa da ƙasa da harsunan duniya, da jami’ar Nazarbayev ta ƙasar Kazakhstan, da jami’ar nazarin ...
A ranar 9 ga watan Afrilu, an shirya bikin rattaba hannu game da daddale yarjejeniyar haɗin gwiwa a tsakanin jami’ar BFSU da ta SOAS a Birtaniya. Mataimakin magajin birnin Beijing Ma Jun ya halarci bikin, gami da yin jawabi a wajen. Zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban BFSU da takwararsa ta SOAS Laura Hammond sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar....
A ranar 11 ga watan Afrilu, jakadan Sri Lanka dake ƙasar Sin Majintha Jayesinghe ya ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin mu’amalar ɗalibai da malamai, da mu’amala a tsakaninsu.
A ranar 13 ga watan Afrilu, jakadan ƙasar Malta dake ƙasar Sin John Busuttil da shugaban jami’ar Malta Alfred J. Vella sun ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian da mataimakinsa Liu Xinlu sun gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakaninsu. Tawagar ta shiga cikin ajin koyar da harshen Malta,...
A ranar 16 ga watan Afrilu, jakadan ƙasar Sweden da ke ƙasar Sin Per Augustsson ya ziyarci BFSU, inda sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da haɗin gwiwar bincike da ƙarfafa mu’amalar malamai da ɗalibai a tsakaninsu. Kafin tattaunawa, Augustsson ya ziyarci kwalejin nazarin harsuna da al’adun ƙasashen Turai,...
A ranar 22 ga watan Maris, an ƙaddamar da taron tattaunawa karo na 9 game da gyare-gyare kan ilmin harsunan waje da samun bunƙasuwa na jami’o’in ƙasar Sin. A yayin taron tattaunawa, an ƙaddamar da dandalin ba da hidimomin harsunan duniya na BFSU. Bisa ƙa’idar samun bunƙasuwa tare, an kafa dandalin ba da hidimomin harsunan waje, da dandalin raya harkokin ilmin ƙasashen waje, da dandalin nazarin ...
Daga ranar 20 zuwa ranar 29 ga watan Maris, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya ziyarci ƙasashen Austriya, da Swiss da Portugal, inda ya ziyarci cibiyar nazarin Jelinek ta Austriya, da jami’ar Vienna, da kwalejin Confucius na jami’ar Vienna, da kwalejin nazarin alaƙar ƙasa da ƙasa da samun bunkasuwa na Swiss, da jami’o’in Porto, da Coimbra, da ULisboa na ...
A ranar 13 ga watan Maris, jakadan ƙasar Portugal dake ƙasar Sin Paulo Jorge Nascimento ya ziyarci BFSU, inda shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian ya gana da shi. Ɓangarorin biyu sun yi tattaunawa game da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen musayar al’adu a tsakaninsu.
A ranar 18 ga watan Maris, jakadar ƙasar Cyprus dake ƙasar Sin Frances Lanitou ta ziyarci BFSU, inda zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban Zhao Gang ya gana da ita. Ɓangarorin biyu sun yi tattaunawa game da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen musayar al’adu a tsakaninsu.