A ranar 26 ga watan Febrairu, jakadan ƙasar Norway dake ƙasar Sin Vebjørn Dysvik ya ziyarci BFSU, inda shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian ya gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da zurfafa ha ɗin gwiwa da ƙara mu’amala a tsakaninsu.
A ranar 26 ga watan Febrairu, kwalejin kasuwancin jami’ar BFSU ya samu saƙon taya murna daga ƙungiyar ɗaliban da suka kammala karatu daga kwalejin kasuwancin Birtaniya, inda ta yawa wa kwalejin kasuwancin BFSU da ya samu amincewa daga ƙungiyar, kuma wa’adin amincewa zai daɗe shekaru 3.Iznin amincewa na BGA ya kasance ɗaya daga cikin manyan tsarin amincewa guda 3 na kwalejojin kasuwancin duniya,...
A ranar 18 ga watan Febrairun shekarar 2025, BFSU ta fara shirya ayyukan da za a ɗauka a zangon karatun da ake ciki.A yayin taron, babban sakataren kwamintin jami’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya bukaci da a ɗauki ƙwararrun matakai don gudanar da ayyukan shekarar 2025. Mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma shugaban BFSU Jia Wenjian ya gabatar da ...
A ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2024, BFSU ta shirya bikin murnar sabuwar shekara ta malaman ƙasashen waje. Zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban jami’ar Zhao Gang ya halarci bikin, gami da yin jawabin fatan alheri. Malaman ƙasashen waje da suka fito daga kwalejojin jami’ar da dangoginsu, da jami’an dake kwalejoji daban daban, da sassan ...
Daga ranar 14 zuwa ranar 23 ga watan Disamba, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Saudiyya da Masar da Aljeriya, inda suka ziyarci jami’ar Yarimar Sultan da ta Gimbiyar Nora bint Abdul Rahman a Saudiyya, da jami‘ar Ain Shams da ta Badr a Masar, da jami’ar Universit d’Alger 3 a Aljeriya,...
Daga ranar 15 zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, an ƙaddamar da taron ƙasa da ƙasa game da koyar da Sinanci a cibiyar tarurrukan Beijing. Taken taron shi ne “Mu’mala da haɗin gwiwa, da ƙirƙiro da sabbin abubuwa”, shugabanni, da ƙwararru da masana na sassan hukumomin ilmi, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da jami’o’in gida da waje, da hukumomin raya harsunan duniya da wakilan masana’antu da ...
A ranar 18 ga watan Nuwamba, an ƙaddamar da taron tattaunawar kwalejojin Confucius na BFSU na shekarar 2024. Taken taron shi ne “Koyi da juna don buɗe sabon babi wajen raya kwalejojin Confucius”, da inganta mu’amala a tsakanin kwalejojin Confucius a tsakaninsu, don samun bunƙasuwa mai inganci. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin BFSU Jia Wenjia ya halarci ...
A ranar 28 ga watan Oktoba, mashawarcin jami’ar Chicago kuma shugaban kwalejin kula da harkokin ɗalibai masu neman digiri na farko John Boyer ya yi jawabi mai taken “Daga jami’ar Chicago, a leƙa yanayin da ake ciki game da karatun Liberal Arts a Amurka”. Kafin aka yi jawabi, sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dnghua ya gana da shi.
A ranar 25ga watan Oktoba, shugaban jami’ar Catholic ta Uruguay Julio Fernandez Techera ya ziyarci BFSU, inda mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian ya gana da shi, inda bangarorin biyu suka tattauna batutuwan kudancin Aurka da alaƙar Sin da ƙasashen yankunan kudancin Amurka, da musayar malamai da ɗalibai a tsakaninsu.