Babban Shafi > Labaru > 正文

Kwalejin kasuwancin BFSU ya samu iznin amincewa daga ƙungiyar BGA

Updated: 2025-03-05

A ranar 26 ga watan Febrairu, kwalejin kasuwancin jami’ar BFSU ya samu saƙon taya murna daga ƙungiyar ɗaliban da suka kammala karatu daga kwalejin kasuwancin Birtaniya, inda ta yawa wa kwalejin kasuwancin BFSU da ya samu amincewa daga ƙungiyar, kuma wa’adin amincewa zai daɗe shekaru 3.

Iznin amincewa na BGA ya kasance ɗaya daga cikin manyan tsarin amincewa guda 3 na kwalejojin kasuwancin duniya, wanda ya nuna cewa, kwalejin kasuwancin BFSU ya samu babban ci gaba wajen haɗin gwiwa da ƙasashen duniya da kyautata ingancin koyarwa.