
A ranar 10 ga watan Disamba, jakadan Finland dake ƙasar Sin Mikko Kinnunen ya ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya gana da shi, inda ɓangarorin biyu suka yi shawarwari game da fadada haɗin gwiwa don sa ƙaimi ga musayar malamai da ɗalibai, da mu’amalar bincike a tsakaninsu.