Babban Shafi > Game da BFSU > Taƙaitaccen bayani
>Taƙaitaccen bayani
>Take da Tambari
>Shugabanni
>Muhimman Adadi
>Jami'a
>Tuntuɓe Mu

Taƙaitaccen bayani

Jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing tana hanyar Xisanhuanbeilu a yankin Haidian da ke birnin Beijing, kuma an raba sashin gabas da na yamma a gefuna biyu na hanyar, kuma jami’ar tana ƙarƙashin shugabancin ma’aikatar kula da ilmin ƙasar Sin, kuma tana ɗaya daga cikin jami’o’i ɗari da Sin za ta ƙoƙarta bunkasuwa a ƙarni na 21, sannan kuma tana ɗaya daga cikin jami’o’in da ke da manyan fannoni masu fiffiko a cikin shirin raya kyawawan jami’o’in da Sin ta gabatar a watan Mayu na shekarar 1998, kana tana ɗaya daga cikin fitattun jami’o’in da Sin take bunƙasuwa yanzu.

Jami’ar BFSU ita cejami’ar koyon harsunan waje ta farko da jam’iyyar kwaminis ta Sin ta kafa, kuma da ma, ita ce, sashin ƙungiyar koyon Rashanci na uku na jami’ar koyon ilmin soji da siyasa don yaƙi da mulkin mallakarJapan ta ƙasar Sin, wadda aka kafa a shekarar 1941, sannan kuma an bunƙasajami’arhar ta zama makarantar koyon harsunan waje ta Yan’an, kuma lokacin da aka kafa ta, tana ƙarƙashin shugabancin kwamitin tsakiyarjam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin. Bayan da aka kafa sabuwar ƙasar Sin, ma’aikatar kula da harkokin waje ta fara shugabantarmakarantar, a shekarar 1954, an canja sunanta zuwa kwalejin koyon harsunan waje na Beijing, a shekarar 1959 ne, aka haɗa ta da kwalejin koyon RashancinBeijing don ya zama sabon kwalejin koyon harsunan wajenBeijing. Bayan shekarar 1980, ma’aikatar kula da ilminSin ta shugabance takai tsaye, a shekarar 1994, an canja sunanta zuwaJami’arKoyonHarsunanWajenTa Beijing.

An amince da buɗe harsunan waje 101 a BFSU, inda kwalejin koyon harsunan Turai da na Asiya da Afrika sun kasance sansanonin nazarin harsunan da ba safai da aka yi amfani da su ba mafi girma aƙasar Sin, kuma sun kasance fannonin karatu na musamman da ma’aikatar ilmi ta amince da su karo na farko. Yanzu, a hannuɗaya, BFSU taƙoƙarta wajen raya fannonin karatu na koyon harsunan waje da adabinsu, a hannuɗayan kuma, aka daidaita bunƙasuwar sauran fannoni kamar adabi da dokoki, da tattalin arziki da harkokin gudanar da ayyuka da sauransu. Tun daga farko zuwa yanzu, an fara buɗe Rashanci, Turanci, Faransanci, Jamusanci, da harshen Spain, da na Poland, da na Czech, da harshen Romaniya, da Japananci, Larabci, da harshen Cambodiya, da na Laos, da harshen Sinhalese, da harshen Malaysiya, da na Sweden, da na Portugal, da na Hungary, da na Albaniya, da na Bulgariya, da harshen Swahili da na Burma, da harshen Indonesiya, da na Italiya, da na Croatiya, da na Serbiya, da harshen Hausa, da na Viemnam, da harshen Thailand, da na Turkiya da na Koriya, da na Slovakiya, da na Finland, da na Ukraine, da na Holland, da na Norway, da na Iceland, da na Danmark, da na Girka, da na Philippines da harshen Hindu, da Urdu, da Hebrew, da Persian, da harshen Sloveniya, da na Estoniya, da na Latviya da na Lithuaniya da harshen Irish, da na Malta da na Bangladesh, da harshen Kazak da Uzbek, Latin, Zulu, da Kyrgyz da Pushutu, da Sanskrit, da Pali da Amharic, da Nepal, da Somali, da Tamil, da Turkmen, da Catala da Yoruba, da harshen Mongoliya, da na Armeniya, da Malagasy, da harshen Georgia, da na Azerbaijan, da Afrikaans, da Macedonian da Tajik, da Setswana da Ndebele da Comorian, da Creole, da Shona, da Tigrinya, da Belarusian, da Maori, da Tangan, da Samoan, da Kurdish, da Bislama, da Dari, da Tetum, da Dhivehi, da Fijian, da Cook Islands Maori, da Kirundi, da Luxembourgish, da Kinyarwanda, da Niuean, da Tok Pisin, da Chewa, da Sesotho, da Sango, da Tamazight, da Javanese, da kuma Punjabi. Jami’a ta bi aƙidar Yan’an don ba da hidimomi gaƙasa. Yanzu, an riga an buɗe harsunan tafiyar da harkokin gwamnatocinƙasashen da suka kafa huldar diflomasiyya daƙasar Sin.

A cikin shekarun nan, jami’ar tanaƙoƙarta wajen yin kwaskwarima ga tsarin horar da ɗalibai, inda aka buɗe ofishin kula da littattafan koyarwa karo na farko a ƙasar Sin. Sannan kuma, an kafa kwalejin BFSU, da kwalejin ƙungiyar ƙasashen duniya, da kwalejin nazarin ilmin koyarwa.A ƙarƙashin tsohon kwalejin nazarin nahiyar Asiya da ta Afrika, an kafa kwalejin nazarin Asiya, da kwalejin nazarin Afrika. Haka kuma, an buɗe cibiyar nazarin manyan harsunan ɗan Adam da fasahohin kwaikwayonƙwalƙwalwa, don ingantaƙwarewar yaɗa labarunƙasa daƙasa. Daɗin dadawa kuma, an buɗeƙwalejin nazarin yaɗa al’adun ƙasar Sin da cibiyar nazarin fasara ta ƙasar da sauran hukumomin nazari. Yanzu, akwai sansanonin nazari na ƙasar Sinda na ƙananan hukumomi 52a BFSU,inda akwai muhimmin sansanin nazarin zamantakewar al’umma da al’adu na ma’aikatar ilmin Sin, da cibiyar nazarin harsunan waje da ilmin Sin, da cibiyar nazarin kimiyya da fasahar harsunan Sin, da sauran sansanonin horaswa na ƙasashe da shiyya-shiyya 4 na ma’aikatarkula dailmin ƙasarSin,wato cibiyar nazarin yankin tsakiya da gabashin Turai, da cibiyar nazarin Japan, da cibiyar nazarin Ingila, da cibiyar nazarin Canada, da ma ragowar cibiyoyi 37 na nazarin shiyya-shiyya daƙasashe da ma’aikatar kula da ilmi ta amince dakafasu. Haka kuma, tana da cibiyoyi 3 na nazarin musayar mutane da al’adu na ma’aikatar kula da ilmi taƙasar wato cibiyar nazarin musayar al’adu da mutane tsakaninƙasashen Sin da Indonesiya, da cibiyar nazarin musanyar al’adu da mutane tsakanin Sin da Faransa, da cibiyar nazarin musayar al’adu damutane dake tsakanin Sin da Jamus. Ban da wannan kuma, akwai muhimmin sansanin nazarin zamantakewar al’umma da kimiyya da fasaha na birnin Beijing, da sansanin nazarin dokoki da ilmi na birnin Beijing. Ban da wannan kuma, BFSU ta shiga jerin farko da ke yalwata harsuna da rubuce-rubucenƙasar Sin, da sansanin nazarin ra’ayin gurguza da ke da halaye musamman na lokacin da muke ciki dakeƙarƙashin shugabancin Xi Jinping a birnin Beijing, kana ankafacibiyar nazarinƙirƙiro da sabbin abubuwa da nazarin ra’ayin gurguzu dake da halayen musamman na jami’o’in Beijing.

Jami’ar ta bugafitattunmujallu guda 4 da ke cikin rukunin CSSCI aƙasar Sinwato mujallarkoyarwa da nazarinharsunan ƙasashen waje, da mujallar nazarin adabin ƙasashen waje, da mujallarnazarindandalin ƙasashen duniya,da mujallar nazarin yanayin da ake ciki game da koyar da harunan waje. Bandawannan kuma,mujallar nazarin ilmi game da koyar da harsunan wajedamujallar koyar da Rashanci a Sin,sun kasance mujallolin da za su shiga cikin jerin CSSCI, ban da wannan kuma, BFSU ta buga sauran mujalloli 7 da harshen Sinanci. Ban da wannan kuma, taɗauki nauyin buga mujallar Turanci ta nazarin harsunan Sin da sauran mujallu 12 da harsunan waje, cikinsu da Turanci da Faransanci, Larabci da Rashanci, da Jamusanci, da harsunan Spainiya daPortugal. Haka kuma, jami’ar tana da sansanin buga littatafai da fitar da faifan bidiyo da na’urorin harsunan waje mafi girma a ƙasar Sin, wato kamfanin kula da harkokin buga littatafan dake shafar koyarwa da nazarin harsunan waje.

BFSU ta buɗe fannonin karatu don neman digirin farko 121, kuma fannonin karatu 47 sun kasance fannin karatu da aka buɗe shi kadai aƙasar Sin. Fannonin karatu 54 sun kasance fitattun fannonin karatunƙasar Sin, yayin da 18 daga cikinsu sun zama fitattun fannonin karatun lardunan Sin, a shekarar 2021, ayyuka 8 sun samu lambobin yabon kyawawan ayyukan koyarwa a jami’o’in birnin Beijing, yayin da salon BFSU wajen horaswa a duniya da harsunan daban daban ya samu lambar yabo ta musamman.

BFSU tana da muhimman fannonin karatu naƙasar Sin guda 4, kuma tana da muhimman fannonin karatu na birnin Beijing guda 7. Jami’ar tana da ikon danka iznin digiri na uku a fannoni guda 2 wato fannin karatu na nazarin harsunan waje da adabi, da fannin karatu na nazarin ilmin kimiyya da tafiyar da harkokin kimiyya da gine-gine, kuma tana da ikon danka iznin digiri na biyu na nazari a fannonin karatu guda 11, wato ilmin dokoki, da ilmin siyasa, da ilmin nazarin tunanin aƙidar Marxism, da ilmin tattalin arziki, da adabin Sinanci, da ilmin harsunan waje da adabi, da ilmin yaɗa labaru da ilmin kimiyya da tafiyar da harkoki da gine-gine da ilmin tafiyar da kasuwanci da masana’antu, da ilmin koyarwa, da ilmin tarihin duniya.Tana da iznin danka digiri na biyu a wajen fannoni karatu 8 wataufassara, da ilmin koyar da Sinanci a ƙasashen waje, dakasuwancin duniya, da haɗa-haɗar kudi, da labaru da yaɗa labaru, da dokoki, da akanta, da tafiyar da harkokin kasuwanci dagine-gine,wandayaƙunshe dailminfannonin karatu guda7na adabi, da tattalin arziki, da tafiyar da harkokin kasuwanci, da dokoki, da koyarwa da tarihida gine-gine.Fannin karatun koyar da harsunan waje da adabi ya yi fice a ƙasar Sin, sannan kuma fannin koyarwa da harsunan waje ya zama fitaccen fannin karatu a birnin Beijing. A sakamakon tantance fannonin karatu na zagaye na 4 da ƙasar Sinta yi, BFSU ta samu maki A+ a cikin fannin karatu na harsunan waje da adabi, kuma ta dau matsayin farko a ƙasar Sin. A shekarar 2023, bisa sakamakon tantance jerin fannonin karatu na duk jami’o’in duniya na QS, an ce, fannonin karatu na harsunanBFSU sun dau matsayi 45 a duk duniya, fannin karatu na harshen Turanci da adabi yadau matsayi na 101 zuwa 150, yayin da ilmin harsunan zamani ya dau matsayi na 151 zuwa 200, wanda ya yi fice a ƙasar Sin.

Yanzu, akwaiɗalibai masu neman digiri na farko 5700, da masu neman digirgiri sama da 3900, kana akwaiɗalibanƙasashen waje 1300 da ke karatu a BFSU.

Jami’ar BFSU taɗora muhimmanci sosai game daƙirƙiro da sabon tsari kula da malamai da ma’aikata, donɗaukaka ingancinsu. Yanzu akwai malamai sama da 1300 a jami’ar, da malamanƙasashen wajekimanin 200 da suka fito dagaƙasashe da yankuna 65, su ma suna aiki a nan. Ban da wannan kuma, jami’ar tana daƙwararru da matasa da ke ba da gudummawa sosai gaƙasar,kana tana daƙwararrun da keƙunshe cikin shirin rayaƙwararru 10000 a fannin zamantakewar al’umma da ra’ayin ilmin fahimtar duniya naƙasar Sin, daƙwararrun waɗanda keƙunshe cikijerinshahararrun malamai 10000 aƙasar Sin, da fitattun furfesa, da sauranƙwararru da masana da dai makamantansu. Kashi 90 cikin 100 na malamai sun taɓaɗalibta aƙasashen waje.Ƙungiyar malamai ta cibiyar nazarin koyarwa harsunan waje ta Sinda ƙungiyar magance matsalolin duniya da horar da ƙwararru a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suntaɓa samun lambobinyabo na fitattunƙungiyoyinmalamainaHuang Danian aƙasar Sin.

BFSU ta nace kan raya jami’a da haɗin gwiwa da fitattun jami’o’in ƙasashen waje, tana mu’amala da haɗin gwiwa da jami’o’i da hukumomin nazari 299 dasukeƙasashe da yankuna 84 a duniya, kuma ta ƙulla dangantakar haɗin gwiwa da jami’ar Brown ta Amurka, da jami’ar Edinburgh ta Birtaniya, da jami’ar Haidelburgh ta Jamus, da jami’ar Moscow ta Rasha, da jami’ar Toronto ta Canada, da kwalejin nazarin harsuna da al’adu na gabashin ƙasashen duniya na Faransa wato INALCO, da jami’ar Tokyo ta Japan, da jami’ar NTU ta Singapore da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, BFSU ta ɗauki nauyin shirya kwalejojin Confucius 23 a ƙasashen Asiya da Turai da Amurka, wanda ya dau matsayi na farko a cikin duk jami’o’in Sin, wasu 7 daga ciknsu sun zama fitattun kwalejojin Confucius. Waɗannan kwalejojin Confucius da BFSU ta shirya sun ƙunshi kwalejin Confucius na jami’ar Nürnberg-Erlangen ta Jamus, da kwalejin Confucius Brussels na ƙasar Belgium, da kwalejin Confucius dake birnin Vienna na ƙasar Austria, da kwalejin Confucoius da ke jami’ar Rome ta ƙasar Italiya, da kwalejin Confucius na Krakow a ƙasar Poland, da kwalejin Confucius na Liege a ƙasar Belgium, da kwalejin Confucius dake Düesseldorf a ƙasar Jamus, da kwalejin Confucius na Eötvös Loránd a ƙasar Hungary, da kwalejin Confucius na Sofia a ƙasar Bulgaria, da kwalejin Confucius dake jami’ar Palacky ta jamhuriyar ƙasar Czech, da kwalejin Confucius na Munich da ke ƙasar Jamus, da kwalejin Confucius na jami’ar Malaya da ƙe kasar Malaysia, da kwalejin Confucius da ke jami’ar Hankuk ta jamhuriyar ƙasar Koriya ta Kudu, da kwalejin Confucius na Barcelona dake ƙasar Spain, da kwalejin Confucius na jami’ar koyon harsuna ta jihar Moscow ta ƙasar Rasha, da kwalejin Confucius na jami’ar da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da kwalejin Confucius na jami’ar London ta Birtaniya, da kwalejin Confucius na jami’ar Tirana dake ƙasar Albaniya, da kwalejin Confucius na jami’ar Göttingen ta ƙasar Jamus, da kwalejin Confucius na jami’ar Oxford Brooks ta Birtaniya, da kwalejin Confucius na jami’ar Colombo dake ƙasar Sri Lanka, da kwalejin Confucius na ESCP Europe dake ƙasar Faransa, da kwalejin Confucius dake makarantar Maryknoll a ƙasar Amurka, da kwalejin Confucius dake jami’arOU a Birtaniya.

A laburarenBFSU, akwai littattafan Sinanci da na harsunan waje da yawansu ya kai kimanin miliyan 1.57, yayin da yawan littattafan da aka samu a Intanet ya wuce miliyan 2.16, kana tana da mujalloli kimanin 1081, da matattarun bayanai na Sinanci da harsunan waje 107, ke nan, an kafa wani tsarin adanan littattafanda suka shafi harsuna da adabi da al’adu.A cikin shekarun nan, bayan da aka ƙara haɓaka fannonin karatu, an kafa tsarin adana littattafan siyasa, da dokoki, da diflomasiyya, da tattalin arziki, da labaru, da tafiyar da ayyuka.Ban da wannan kuma, jami’ar tanaƙoƙarta raya harkokin sadarwa, don kafa wani tsarin sadarwa a bayyane, na zamani da ke iyaƙirƙiro da sabbin tunani, kuma ta samu muhimman sakamako kamar shafin Intanet da harsunan waje da yawa, da shafin Intanet na BFSU na zaman,da dandalin manhajar kiɗiɗɗiga da dai sauransu.Ban da wannan kuma, an fara kafa azuzuwa da muhallin karatu na zamani. A shekarar 2021, an kammala aikin gwaji na horar da malaman jeri na farko na ma’aikatar kula da ilmin Sin, kuma an fidda shawarar raya malamai ta fasahohin zamani. An kafa ɗakunan nune-nunen harsunan duniya da ƙago wuraren da ke da halayen musamman na harsuna da al’adu, kuma an kafa sabon ɗakin nune-nunen tarihin BFSU, don waiwaye adon tafiyar gina BFSU daga duk fannoni.