
A ranar 18 ga watan Febrairun shekarar 2025, BFSU ta fara shirya ayyukan da za a ɗauka a zangon karatun da ake ciki.
A yayin taron, babban sakataren kwamintin jami’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya bukaci da a ɗauki ƙwararrun matakai don gudanar da ayyukan shekarar 2025. Mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma shugaban BFSU Jia Wenjian ya gabatar da jawabi mai taken “A nace kan gudanar da matakai don raya fitaciyyar jami’ar BFSU mai inganci a duniya”, inda ya gabatar da fannoni 7 da za a inganta su.
A wajen mu’amala da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, an yi kira da a ƙoƙarta wajen raya mu’amala da haɗin gwiwa, don sa kaimi ga samar da sakamako masu gamsarwa, da inganta haɗin gwiwa da sauran jami’o’n ƙasashen duniya, don raya ƙawacen jami’o’in harsunan wajen ƙasashen duniya, da amfani da dandalin tattaunawa da taron ƙara-wa-juna sani don lalubo bakin zaren raya jami’o’in harsunan waje a ƙasashen duniya.