Babban Shafi > Labaru > 正文

Jakadan ƙasar Uruguay ya ziyarci BFSU

Updated: 2026-01-09

A ranar 24 ga watan Disamba, jakadan ƙasar Uruguay dake ƙasar Sin Aníbal Cabral ya ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jam’ar BFSU Jia Wenjian da zaunannen mamban kwamitin jam’yyar kwaminisancin jami’ar kuma mataimakin shugaban jami’ar Zhao Gang sun gana da shi.

Shugaban Jia ya gabatar da halin dake ciki da mu’amalar ƙasashen duniya, da fannin raya harshen Spain da binciken nahiyar Latin Amurka, da waiwayi baya game da mu’amala da tuntuɓawar dake tsakanin BFSU da shugabannin Uruguay da abokan aiki a jami’o’in ƙasar ta sahihiyar zuciya. Ya bayyana cewa, BFSU ta ɗora muhimmanci sosai game da mu’amala da Uruguay da sauran ƙasashen Latin Amurka, kuma yana fata kara fahimtar juna da sada zumunta game da haɗin gwiwa a fannin ilmi da tattaunawa a tsakanin matasa.

A nasa ɓangare kuma, Cabral ya yi farin ciki da sake ziyarar BFSU. Ya yaba wa muhimmiyar rawar da BFSU ta taka wajen horar da ɗalibai, da sa ƙaimi ga mu’amala da ke tsakanin mu’amalar al’adu a tsakaninsu. Yana sa rai za a inganta haɗin gwiwar ɓangarorin biyu, da raya mu’amalar matasa da bincike, da inganta mu’amala a fannoni ilmi da al’adu, don cusa sabbin abubuwa game da raya alaƙar ƙasashen biyu.