Yayin da aka yi mu’amala tsakanin bambancin al’adun ƙasashen duniya, za a haɓaka al’adu na ko wace ƙasa na ƙasashen duniya. A halin da ake ciki yanzu, watau yayin da ake fuskanta sauye-sauyen da ba a taɓa ganin irinsa ba cikin shekaru 100 da suka gabata, ana bukatar mu’amala da tattaunawa tsakanin bambancin al’adun ƙasashen duniya. Dalilin da ya sa aka tsara shirye-shiryen hotunan bidiyo na “Koyi da Juna, Sin da Ƙasashen Duniya” shi ne don ƙoƙarin mu’amala tsakanin mabanbanta al’adun ƙasashen duniya, da samu irin yanayi na koyi da juna da samun jituwa tsakanin ƙasashen duniya, ta hakan za a ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen duniya wajen raya al’adunsu. Ƙwararru da masana ta fuskar al’adu na ƙasashe 12 na kokarin mu’amala tsakaninsu, don ganewa idanunsu mu’amala tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen duniya.
I
II
III
IV
V
VI
VII
VIII
IX
X