Babban Shafi > Labaru > 正文

Shugaban BFSU Li Hai ya halarci taron tattaunawa karo na biyu game da ilmin Sin da Faransa

Updated: 2025-12-17

A ranar 5 ga watan Disamba, ma’aikatar kula da ilmin Sin da ma’aikatar kula da jami’o’i, da bincike, da nazarin sararin sama sun shirya taron tattaunawa karo na biyu game da samun bunƙasuwar ilmin Sin da Faransa. Bisa goron gayyata da aka yi, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Li Hai ya halarci taron, inda ya yi jawabi mai take “Raya dauwamammen ci gaba game da tsarin horar da ɗalibai don samu makoma mai haske.”