Babban Shafi > Labaru > 正文

Jakadan New Zealand ya ziyarci BFSU

Updated: 2025-12-17

A ranar 12 ga watan Disamba, jakadan New Zealand a ƙasar Sin Jonathan Austin ya ziyarci BFSU. Saktaren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Li Hai ya gana da Austin, inda ɓangarorin biyu suka yi shawarwari game da musanyar malamai da ɗalibai, da gudanar da bincike, da raya harshen Maori da sauran harsunan yankin kudancin tekun kudancin Fasific da dai sauransu.