
A ranar 4 ga watan Fabrairu, shugaban ƙasar Uruguay Yamandu Orsi ya kai ziyara a BFSU, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Li Hai da mataimakin sakataren kwamitin kuma shugaban BFSU Jia Wenjian, da zaunannen mamban kwamitin kuma mataimakin shugaban jami’ar Zhao Gang, da jakadan Sin a ƙasar Uruguay Huang Yazhong, da ƙaramin jakadan Zhang Wenwei a sashen kula da kudancin Amurka da tekun Caribbean na ma’aikatar kula da harkokin wajen Sin, da mataimakin direktan sashen kula da haɗin gwiwa da mu’amala na ma’aikatar kula da ilmin Sin Zhang Jin sun halarci bikin.
Orsi ya taɓa raka tsohon shugaban ƙasar Uruguay José Mujica don dasa itacen sada zumunta a jami’ar a shekarar 2013. A wannan rana da safe, shugabannin jami’ar Li Hai da Jia Wenjian sun raka shugaban Orsi don dasa sabon itace.
Daga bisani kuma, Orsi ya raka shugabanni don yin mu’amala da malamai da ɗalibai masu nazarin harshen Spain a jami’o’i 16 na Beijing. Shugaban Jia ya shugabanci bikin.
A madadin jami’ar, Li Hai ya yi maraba da Orsi. Ya bayyana cewa, BFSU tana haɗin gwiwa da Uruguay a kullum, kuma tana sa ran ƙarfafa mu’amala da haɗin gwiwa da jami’o’i da hukumomin nazari, don ƙara horar da matasa dake sanin harsuna da al’adun ƙasashen biyu da sada zumunta a tsakanainsu.
Orsi ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, mu’amala a fannin nazari ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa amincewar juna wajen ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu, da yauƙaƙa mu’amalar nazari a tsakanin ƙasashen biyu da raya alaƙar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen kudancin Amurka. Ƙarfafa mu’amalar jama’a zai aza harsashi wajen sa ran ga ɓangarorin biyu don koyon fasahohi, da ƙarfafa haɗin gwiwa da tattaunawa don sa ƙaimi ga samar da zaman lafiya da samun bunƙasuwa.
Bayan jawabin, Orsi ya yi mu’amala da malamai da ɗalibai, sannan sakataren Li Hai ya miƙa zane-zanen itacen sada zumunta tsakanin Sin da Uruguay da ɗaliban BFSU suka yi ga shugaban Orsi.
Kafin bikin, Orsi ya duba sakamakon koyarwa da mu’amala da sashen harshen Spain na BFSU ya samu, kuma ya yi rubuce-rubuce don taya murna gare shi. Ɗaliban BFSU sun yi waƙe-waƙe da sauran wasanni, inda suka samu karɓuwa daga ’yan kallo.
Ministan harkokin wajen Uruguay Mario Lubetkin, da jakadan Uruguay a ƙasar Sin Anibal Cabral, da sauran mambobin tawagar sun halarci bikin.