Babban Shafi > Labaru > 正文

Li Hai ya zama sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU

Updated: 2025-11-29

A ranar 19 ga watan Nuwamba, ma’aikatar kula da harkokin ilmin Sin ta sanar da cewa, Li Hai zai zama sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU, Wang Dinghua ba zai ci gaba da zama sakataren ba. Mataimakin ministan ilmi kuma mai sa ido game da harkokin karatu na ma’aikatar kula da ilmin ƙasar Sin Wang Jiayi ya halarci taro gami da yin jawabi. Mataimakin direktan maikatar kula da harkokin ilmin Sin Ge Yuanjie da mataimakin sakataren kwamitin ilmin birnin Beijing Yu Chengwen ya halarci taro. Shugaban jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci taron.