Yayin da aka yi mu’amala tsakanin bambancin al’adun ƙasashen duniya, za a haɓaka al’adu na ko wace ƙasa na ƙasashen duniya. A halin da ake ciki yanzu, watau yayin da ake fuskanta sauye-sauyen da ba a taɓa ganin irinsa ba cikin shekaru 100 da suka gabata, ana bukatar mu’amala da tattaunawa tsakanin bambancin al’adun ƙasashen duniya. Dalilin da ya sa aka tsara shirye-shiryen hotunan bidiyo ...
Daga ranar 11 zuwa ranar 13 ga wata, an shirya taron kwamitin haɗin gwiwar ilmi tsakanin ƙasashen Sin da Belarus kuma taron ministocin ilmi karo na farko tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Asiya ta tsakiya, da taron shekara-shekara na jami’ar ƙungiyar SCO na 2025, da taron ministocin ilmi na mambobin ƙungiyar SCO karo na 9 a birnin Urumqi da ke jihar Xinjiang, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren ...
Daga ranar 16 zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Kazakhstan da Uzbekistan da Kyrgyzstan, inda ya ziyarci jami’ar Al-Farabi, da jami’ar Ablai Khan dake nazarin alaƙar ƙasa da ƙasa da harsunan duniya, da jami’ar Nazarbayev ta ƙasar Kazakhstan, da jami’ar nazarin ...
A ranar 9 ga watan Afrilu, an shirya bikin rattaba hannu game da daddale yarjejeniyar haɗin gwiwa a tsakanin jami’ar BFSU da ta SOAS a Birtaniya. Mataimakin magajin birnin Beijing Ma Jun ya halarci bikin, gami da yin jawabi a wajen. Zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban BFSU da takwararsa ta SOAS Laura Hammond sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar....
A ranar 11 ga watan Afrilu, jakadan Sri Lanka dake ƙasar Sin Majintha Jayesinghe ya ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin mu’amalar ɗalibai da malamai, da mu’amala a tsakaninsu.
A ranar 13 ga watan Afrilu, jakadan ƙasar Malta dake ƙasar Sin John Busuttil da shugaban jami’ar Malta Alfred J. Vella sun ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian da mataimakinsa Liu Xinlu sun gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakaninsu. Tawagar ta shiga cikin ajin koyar da harshen Malta,...
A ranar 16 ga watan Afrilu, jakadan ƙasar Sweden da ke ƙasar Sin Per Augustsson ya ziyarci BFSU, inda sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da haɗin gwiwar bincike da ƙarfafa mu’amalar malamai da ɗalibai a tsakaninsu. Kafin tattaunawa, Augustsson ya ziyarci kwalejin nazarin harsuna da al’adun ƙasashen Turai,...
A ranar 22 ga watan Maris, an ƙaddamar da taron tattaunawa karo na 9 game da gyare-gyare kan ilmin harsunan waje da samun bunƙasuwa na jami’o’in ƙasar Sin. A yayin taron tattaunawa, an ƙaddamar da dandalin ba da hidimomin harsunan duniya na BFSU. Bisa ƙa’idar samun bunƙasuwa tare, an kafa dandalin ba da hidimomin harsunan waje, da dandalin raya harkokin ilmin ƙasashen waje, da dandalin nazarin ...
Daga ranar 20 zuwa ranar 29 ga watan Maris, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya ziyarci ƙasashen Austriya, da Swiss da Portugal, inda ya ziyarci cibiyar nazarin Jelinek ta Austriya, da jami’ar Vienna, da kwalejin Confucius na jami’ar Vienna, da kwalejin nazarin alaƙar ƙasa da ƙasa da samun bunkasuwa na Swiss, da jami’o’in Porto, da Coimbra, da ULisboa na ...