Babban Shafi > Labaru > 正文

Ministan wasanni da fasaha da al'adun Afirka ta Kudu ya ziyarci BFSU

Updated: 2025-12-17

A ranar 3 ga watan Disamba, ministan dake kula da wasanni da fasaha da al’adun ƙasar Afirka ta Kudu Gayton Mckenzie ya shugabanci tawaga don kai ziyara a BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian, da zaunannen mamban kwamitin kuma mataimakin shugaban BFSU Liu Xinlu sun yi shawarwari da tawaga, inda ɓangarorin biyu suka tattauna haɗin gwiwa game da mu’amalar malamai da ɗalibai da gudanar da bincike cikin haɗin gwiwa da fasarar adabi da nazarin fasahohi da dai sauransu.