
A ranar 23 ga watan Yuni, shugaban majalisar dokokin ƙasar Thailand Wan Muhamad Noor Matha ya ziyarci BFSU. Sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da zaunannen mamban jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Zhao Gang ya gana da shi.
Wang Dinghua ya bayyana cewa, a cikin shekaru 50 da suka gabata, bayan da ƙasashen Sin da Thailand suka ƙulla alaƙar dake tsakaninsu, alaƙar da ke tsakaninsu ta ƙara yauƙaƙa a tsakaninsu. Wannan ziyara za ta taimaka wajen zurfafa fahimtar juna dake tsakaninsu, da sada zumunta a tsakaninsu. Ana fata za a ci gaba da yalwata haɗin gwiwa, da haɗa hannu wajen horar da ƙwararru. Wan Muhamad Noor Matha ya jinjina gudummawar da BFSU ta bayar wajen sada zumunta tsakaninsu, kuma ya yi maraba da mu’amala da tattaunawa tsakanin matasa a tsakaninsu.
Daga bisani kuma, Wan Muhamad Noor Matha ya yi shawarwari da malamai da ɗaliban BFSU game da alaƙar dake tsakanin ƙasashen Sin da Thailand, da musanyar ilmi, da raya harkokin matasa da dai sauransu.