Babban Shafi > Labaru > 正文

Mataimakin ministan ilmin Malaysia ya ziyarci BFSU

Updated: 2025-06-27

A ranar 18 ga watan Yuni, mataimakin ministan ilmin Malaysia Wong Kah Who ya ziyarci BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian da mamban zaunannen kwamitin kuma mataimakin shugaban BFSU Zhao Gang ya gana da shi.

Shugaban Jia ya bayyana halin da ake ciki wajen horar da ƙwararru da mu’amalar ƙasashen waje, da raya fannonin karatu, kuma yana fata za a yi amfani da wannan ziyara don inganta haɗin gwiwa da ɓangarorin daban daban na ƙasar Malaysia, don ba da babbar gudummawa wajen raya harkokin ilmi da musanyar al’adu a tsakanin ƙasashen biyu da ƙasashen shiyya-shiyya. Ministan Wong ya bayyana cewam ma’aikatar kula da harkokin ilmin Malaysia ta ɗora muhimmanci sosai game da mu’amala da tattaunawa tsakaninsu da BFSU, ana fata ƙara haƙiƙanin haɗin gwiwa a wajen nazarin harsuna, da mu’amalar malamai, da musayar ɗalibai, da shirya taron bincike.

Daga bisani kuma, ministan Wong ya ziyarci cibiyar nazarin harshen Malaysia na kwalejin nazarin ilmin Asiya.