Babban Shafi > Labaru > 正文

BFSU ta daddale yarjejeniyar haɗin gwiwa da SOAS

Updated: 2025-04-23

A ranar 9 ga watan Afrilu, an shirya bikin rattaba hannu game da daddale yarjejeniyar haɗin gwiwa a tsakanin jami’ar BFSU da ta SOAS a Birtaniya. Mataimakin magajin birnin Beijing Ma Jun ya halarci bikin, gami da yin jawabi a wajen. Zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban BFSU da takwararsa ta SOAS Laura Hammond sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar.