Babban Shafi > Labaru > 正文

Shugaban BFSU ya kai ziyarar aiki a ƙasashe 3 a yankin tsakiyar Asiya

Updated: 2025-05-07

Daga ranar 16 zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Kazakhstan da Uzbekistan da Kyrgyzstan, inda ya ziyarci jami’ar Al-Farabi, da jami’ar Ablai Khan dake nazarin alaƙar ƙasa da ƙasa da harsunan duniya, da jami’ar Nazarbayev ta ƙasar Kazakhstan, da jami’ar nazarin abubuwan gado na al’adu da yawon shaƙatawar ƙasa da ƙasa ta hanyar Siliki, da jami’ar Alisher Navoiy ta harsunan waje da adabi, da jami’ar Mirzo Ulugbek ta Uzbekistan, da jami’ar KNU da jami’ar Bishkek ta ƙasar Kyrgyzstan, inda suka tattauna mu’amala da haɗin gwiwa a tsakaninsu, kuma sun ziyarci ofishin jakadancin Sin da ke ƙasar Kazakhstan, da ƙaramin ofishin jakadancin Sin da ke birnin Almaty, da ofishin jakadancin Sin da ke ƙasar Uzbekistan, da ofishin jakadancin Sin dake ƙasar Kyrgyzstan, da ma’aikatar ilmi da kimiyya ta ƙasar Kyrgyzstan, kana sun yi nazari game da kamfanin haɗin gwiwar raya masana’antun Pengsheng, da aikin layin dogo na jiragen ƙasa na Sin da Kyrgyzstan, da Uzbekistan.

Wannan karo na farko da jami’ar BFSU ta tura tawaga don kai ziyara a ƙasashen Uzbekistan da Kyrgyzstan. Tawagar BFSU ta cimma ra’ayi guda da takwarorinta a waɗannan ƙasashe 3 game da inganta aikin koyarwa da horar da ƙwararru, da gudanar da bincike cikin haɗin gwiwa da manyan jami’o’i masu nazari da koyarwa, kuma sun horar da fitattaun masu aikin tafinta tsakanin harsunan ƙasashen tsakiyar Asiya da Rashanci, da Sinanci, da jawo hankalin ɗalibai da malamai don su yi karatu a ƙasar Sin, kuma an daddale yarjejeniyar fahimtar juna game da haɗin gwiwa a fannoni da yawa.