
A ranar 26 ga watan Yuli, shugaban gwamnatin yankin Catalonian na ƙasar Spainiya Salvador Illa ya shugabanci tawaga don kai ziyara a BFSU. Shugaban jami’a kuma mataimakin sakataren kwamitin kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya gana da tawaga, direktan sashen kula da tuntuɓawar ƙasashen waje na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Wang Huayong da jakadan Spainiya a ƙasar Sin Marta Betanzos sun halarci taron shawarwari. Ɓangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi game da alaƙar ɓangarorin biyu, da horar da ƙwararru, da haɗin gwiwa a kan mu’amalar harshe da al’adu da sauran batutuwa.