Babban Shafi > Labaru > 正文

Shugaban BFSU ya shugabanci tawaga don halartar taron ministocin ilmi karo na farko na ƙasar Sin da ƙasashen Asiya ta tsakiya

Updated: 2025-05-27

Daga ranar 11 zuwa ranar 13 ga wata, an shirya taron kwamitin haɗin gwiwar ilmi tsakanin ƙasashen Sin da Belarus kuma taron ministocin ilmi karo na farko tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Asiya ta tsakiya, da taron shekara-shekara na jami’ar ƙungiyar SCO na 2025, da taron ministocin ilmi na mambobin ƙungiyar SCO karo na 9 a birnin Urumqi da ke jihar Xinjiang, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya halarci tarurruka.

A yammacin ranar 11 ga wata, an gudanar da taro karo na 8 na kwamitin haɗin gwiwar ilmi tsakanin ƙasashen Sin da Belarus. Mataimakin ministan ilmin Sin Wu Yan da ministan ilmin Belarus Andrei I. Ivanets sun shugabanci taro. A yayin taron, Jia Wenjian da takwaransa na jami’ar BSU Andrei D. Karol da takwararsa ta jami’ar MSLU Natalia Lapteva sun sanar da ƙaddamar da cibiyar mu’amala tsakanin ƙasashen Sin da Belarus.

A safiyar ranar 12 ga watan Mayu, an ƙaddamar da taron ministocin ilmi karo na farko na ƙasashen Sin da Asiya ta tsakiya, inda ministan ilmin Sin Huai Jinpeng ya yi muhimmin jawabi. A yayin bikin, Prof. Jia Wenjian da ministar ilmi da kimiyya Kyrgyzstan Dogdurkul Kendirbaeva sun daddale yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin BFSU da ma’aikatar kula da ilmi da kimiyyar ƙasar.

Daga ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Mayu, an gudanar da taron shekara-shekara na jami’ar ƙungiyar SCO, shugaban jami’ar BFSU Jia Wenjian ya halarci bikin ƙaddamar da taron, shugabar kwalejin nazarin Rashancin jami’ar BFSU Dai Guiju ta yi jawabi a yayin taron tattaunawa game da ilmin koyarwa ta kimiyya.

A safiyar ranar 13 ga watan Mayu, an gudanar da taron ministocin ilmin ƙungiyar SCO. A yayin taron, Jia Wenjian ya ƙaddamar da ƙungiyar haɗin gwiwa game da ilmin digital na ƙungiyar SCO, da cibiyar ƙirƙiro da sabbin tunani na Sin da ƙungiyar SCO.