
Daga ranar 22 ga watan Yuni zuwa ranar 1 ga watan Yuli, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya ziyarci ƙasashen Rwanda, da Uganda, da Kenya, inda ya ziyarci jami’ar Rwanda da ta Makerere,da kwalejin nazarin kimiyyar Luyanzi, da cibiyar sa ido game da nazarin bunƙasuwar Uganda, da jami’ar Kenyatta, da ta Nairobi da sauran jami’o’i da cibiyoyin nazari, don tattauna mu’amala da haɗin gwiwa da jami’ar BFSU. Haka kuma, shugaban Jia ya ziyarci ofisoshin jakadancin Sin da ke Rwanda, da Uganda, da Kenya, kuma ya gana da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a Rwanda, da bincike ofishin CCECC a ƙasar Rwnada, da ayarin likitocin Sin da ke Rwanda, da kamfanin Star Times dake Uganda, da kamfanin CCECC a ƙasar Kenya, da sashen Afirka na kamfanin dillancin labarun Xinhua, da ofishin kamfanin CRBC dake Kenya, kuma an shirya taron ƙara-wa-juna sani da cibiyar sa ido game da nazarin bunƙasuwar Uganda da jami’ar Nairobi, haka kuma ya zanta da manema labaru. Wannan shi ne karo na farko da BFSU ta tura tawaga ga ƙasashen Uganda Rwanda, don inganta aikin koyar da harsuna da al’adun ƙasashen Afirka, da horar da ƙwararru, da gudanar da bincike cikin haɗin gwiwa wajen binciken ƙasashen duniya da shiyya-shiyya, da fadada haɗin gwiwa tsakanin jami’a da kamfanoni da samar da guraben ayyukan gwaji ga ɗalibai, inda aka daddale yarjejeniyoyin fahimtar juna da abokan BFSU a ƙasashe 3 dake gabasin Afirka, da zurfafa amincewar juna, da yalwata haɗin gwiwa, kuma an samu nasarar wannan ziyara.