Babban Shafi > Labaru > 正文

Shugaban BFSU ya halarci taron koyar da Sinanci na duniya

Updated: 2024-11-25

Daga ranar 15 zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, an ƙaddamar da taron ƙasa da ƙasa game da koyar da Sinanci a cibiyar tarurrukan Beijing. Taken taron shi ne “Mu’mala da haɗin gwiwa, da ƙirƙiro da sabbin abubuwa”, shugabanni, da ƙwararru da masana na sassan hukumomin ilmi, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da jami’o’in gida da waje, da hukumomin raya harsunan duniya da wakilan masana’antu da jakadu na ƙasashe da yankuna sama da 160 kimanin 2000 sun halarci taron. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian da mataimakinsa Liu Xinlu sun halarci taron. A yayin taron ƙara-wa-juna sani na zagayowar shekaru 20 da kafuwar kwalejin Confucius, shugaban Jia ya yi jawabi mai take “Koyi da juna, don buɗe sabon babin raya Confucius.”