A ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2024, BFSU ta shirya bikin murnar sabuwar shekara ta malaman ƙasashen waje. Zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban jami’ar Zhao Gang ya halarci bikin, gami da yin jawabin fatan alheri. Malaman ƙasashen waje da suka fito daga kwalejojin jami’ar da dangoginsu, da jami’an dake kwalejoji daban daban, da sassan kula da harkokin jami’ar da wakilan malamai da ɗalibai sama da 100 sun halarci bikin.
A yayin bikin, an miƙa lambobin yabo na karramawa malaman ƙasashen waje 4 da suka kwashe shekaru sama da 10 suna koyarwa a ƙasar Sin. Furfesa Charassri Jiraphas daga sashen Thai na kwalejin nazarin Asiya, da Furfesa Wang Dehong ɗan ƙasar Singapore da ke koyarwa a kwalejin nazarin kasuwacin duniya, da Malam Chun Ethan Forbes ɗan ƙasar Australiya da ke aiki a kwalejin nazarin kasuwancin duniya sun bayar da jawabi ɗaya bayan ɗaya.
Daga bisani kuwa, malamai da ɗalibai sun nuna wasanni masu ƙayatarwa ga baƙi dake wuri. Malaman gida da waje sun yi murnar zuwa sabuwar shekara.