
A ranar 11 ga watan Oktoba, shugabar majalisar dokokin Cyprus Demetriou ta shugabanci tawaga don kai ziyara a BFSU gami da yin jawabi a wurin. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian ya gana da ita.
Bayan da ta yi jawabi, Demetriou da shugaban Jia sun yi shawarwari da malamai da ɗalibai, kana Demetriou ta amsa tambayar da aka yi mata.