Daga ranar 22 ga watan Satumba zuwa ranar 2 ga watan Oktoba, sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Amurka da Cuba, da Panama. Mambobin tawagar sun halarci taron tattaunawar shugabannin jami’o’in Sin guda 10 da na Amurka guda 10, kuma sun ziyarci jami’o’in Amurka NU da UChicago da SBU da NYU da Columbia da Vandy da hedkwatar M.D.D., da jami’ar UH ta Cuba, da jami’ar Panama, da kwalejin Confucis na jami’ar Panama, kana sun ziyarci ƙaramin ofishin jakadancin Sin da ke birnin New York da sashen dake kula da harkokin yankin arewacin Amurka na kamfanin dillancin labaru na Xinhua, da ofishin jakadancin Sin da ke kasar Cuba, kana sun gana da abokan karatun BFSU a ƙasashen Amurka da Cuba da Panama.