Daga ranar 14 zuwa ranar 23 ga watan Disamba, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Wenjian ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Saudiyya da Masar da Aljeriya, inda suka ziyarci jami’ar Yarimar Sultan da ta Gimbiyar Nora bint Abdul Rahman a Saudiyya, da jami‘ar Ain Shams da ta Badr a Masar, da jami’ar Universit d’Alger 3 a Aljeriya, don karfafa mu’amala a tsakaninsu, kana sun ziyarci cibiyar nazarin mashigin tekun Gulf ta Saudiyya, da cibiyar nazari da mu’amalar ilmi ta ƙasar, kana sun yi tattaki zuwa sashen fasara na kwamitin ƙolin nazarin al’adun Masar, da kwamitin sada zumunta na Aljeriya da Sin. Sun inganta haɗin gwiwar sada zumunta da cibiyoyin nazari da ƙungiyoyi. Ban da wannan kuma, sun ziyarci reshen kamfanin Huawei a Saudiyya, da ofishin jakadancin Sin da ke wadannan ƙasashe, gami da mu’amala da jami’an diflomasiyya. Haka kuma, sun gana da ɗaliban da abokan karatu na BFSU a waɗannan ƙasashe.