Babban Shafi > Labaru > 正文

An ƙaddamar da taron tattaunawar kwalejojin Confucius na BFSU na 2024

Updated: 2024-11-25

A ranar 18 ga watan Nuwamba, an ƙaddamar da taron tattaunawar kwalejojin Confucius na BFSU na shekarar 2024. Taken taron shi ne “Koyi da juna don buɗe sabon babi wajen raya kwalejojin Confucius”, da inganta mu’amala a tsakanin kwalejojin Confucius a tsakaninsu, don samun bunƙasuwa mai inganci. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin BFSU Jia Wenjia ya halarci bikin ƙaddamar da taron. Shugabannin kwalejojin Confucius 22 na ƙasashe 18 kimanin 100 sun halarci bikin buɗe taron. A yayin taron kwanaki biyu, wakilan kwalejojin Confucius sun tattauna batutuwan horar da malamai, da fadada haɗin gwiwa, da raya sabbin ayyuka.