A ranar 23 ga watan Fabrairu, BFSU ta fara tsara ayyukan zangon karatu na shekarar 2022.Babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Wang Dinghua da mataimakinsa kuma shugaban jami’ar Yang Dan, da mataimakin sakataren jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia Wenjian, da zaunannen mamban jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma mataimakin shugaban jami’ar S...
A ranar 14 ga wata, ma’aikatar kula da ilmi, da ma’aikatar kula da kuɗi, da kwamitin yin gyare-gyare da samun bunƙasuwa na Sin sun fidda takardar jin ra’ayoyin raya fitattun jami’o’in duniya a Sin da kyawawan fannonin karatu a ƙasar, inda aka bayar da jerin sunayen jami’o’i da fannonin nazari da za a raya a zagaye na biyu. A zagaye na farko, BFSU ta riga ta kasance cikin fitattun ja...
Mun haɗu gaba ɗaya don amfanin gabaZumar ƙauna ta duniya,Kamar dusar ƙanƙara a ƙasa.Tashi sama,Mun ga yadda ta faɗa ƙasa.Makoma a gabanmu,Muna jiran zuwanta.Tashi sama,Aljanna za ta nuna ma.Ƙaunar muke buƙata,Sai mu ƙara yin haɗin kai.Mun haɗu don amfanin gaba,Ni da kai,Mu yi tattaki!Ƙaunar muke buƙata,Sai mu ƙara yin haɗin kai.Mun haɗu domin amfanin gaba,Ni da kai,Mu yi t...
Bisa labarin da kwamitin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ya bayar, an ce, Samuel Uduigowme Ikpefan mai shekaru 30 da haihuwa, ya kammala gasarsa a wasannin Olympics na bana, inda ya samu matsayi na 73 a gasar gudu kan dusar ƙanƙara a daji ta gajeren zango, kuma bai kammala wasanni ba cikin gasar gudu kan dusar ƙanƙara a daji mai nisan kilomita 15. Ikpefan ya zama ɗa...
Bisa labarin da shafin Internat na gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta bayar a ranar 10 ga wata, a rana ta farko bayan da aka kammala bikin sabuwar shekara ta Sinawa, an buga waya ga Gao Xiaofan, bayan da ta gama da aiki, ƙarfe 6 ya yi. A wannan rana, watau ranar haihuwarta, a matsayinta na mai aikin sa kai na jami’ar BFSU, ta ɗauki nauyin karɓar tawagar Ukraine ta gasa...
A ranar 9 ga watan Fabrairu, bisa labarin da jaridar Economic Daily ta Sin ta bayar, an ce, a yayin taron manema labarun da kwamitin gasar wasannin Olympics na duniya da kwamitin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing suka shirya, shugaban kula da tsare-tsaren kwamitin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing Li Sen ya taƙaita nasarorin da gasar wasannin Olympics ta s...
Bisa labarin da kafofin yada labarun ƙasar Sin CNS ya bayar, an ce, an gudanar da gasar samun izinin shiga gasar ƙarshe ta wasan gudu a kan dusar ƙanƙara cikin ’yanci ta mata ta hanyar tsalle daga dandalin gasar Olympics a lokacin sanyi ta 2022, inda ’yar wasan ƙasar Sin Gu Ailing ta halarci gasar. Bisa labarin da aka samu, an ce, tun daga shekarar 2019, Gu Ailing ta fara shiga gasa a ...
Bisa labarin da shafin Internet na Tianshan na ƙasar Sin ya bayar, an ce, a yammacin shekaranjiya 5 ga watan Fabarairu, Dinigeer Yilamujiang da abokiyar wasanninta a ƙungiyar ƙasar Sin Bayani Jialin suka fara wasannin gudu a kan dusar ƙanƙara na ƙetaren daji na gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing. Haka kuma, wannan shi ne karo na farko da aka samu ’yan wasan daga birnin Altay da...
A ranar 18 ga watan Janairu,an kaddamar da bikin tura matasa masu aikin sa kai na BFSU zuwa gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da gasar wasannin Olympics ta nakasassu. Haka kuma, wannan biki ya kasance bikin fara ba da hidimomi da harsunan daban daban na Beijing a hukunce. Mataimakin shugaban kula da sashen tuntubawar waje na kwamintin shirya wasannin Olympics na Beijing W...