
A ranar 14 ga wata, ma’aikatar kula da ilmi, da ma’aikatar kula da kuɗi, da kwamitin yin gyare-gyare da samun bunƙasuwa na Sin sun fidda takardar jin ra’ayoyin raya fitattun jami’o’in duniya a Sin da kyawawan fannonin karatu a ƙasar, inda aka bayar da jerin sunayen jami’o’i da fannonin nazari da za a raya a zagaye na biyu. A zagaye na farko, BFSU ta riga ta kasance cikin fitattun jami’o’i da kyawawan fannonin karatu da za a raya, a wannan karo, aka sake shiga cikin jerin sunayen, kuma za a ƙoƙarta wajen raya fannin karatun nazarin harsuna da adabin kasashen waje.