Bisa labarin da shafin Internat na gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta bayar a ranar 10 ga wata, a rana ta farko bayan da aka kammala bikin sabuwar shekara ta Sinawa, an buga waya ga Gao Xiaofan, bayan da ta gama da aiki, ƙarfe 6 ya yi. A wannan rana, watau ranar haihuwarta, a matsayinta na mai aikin sa kai na jami’ar BFSU, ta ɗauki nauyin karɓar tawagar Ukraine ta gasa...
A ranar 9 ga watan Fabrairu, bisa labarin da jaridar Economic Daily ta Sin ta bayar, an ce, a yayin taron manema labarun da kwamitin gasar wasannin Olympics na duniya da kwamitin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing suka shirya, shugaban kula da tsare-tsaren kwamitin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing Li Sen ya taƙaita nasarorin da gasar wasannin Olympics ta s...
Bisa labarin da kafofin yada labarun ƙasar Sin CNS ya bayar, an ce, an gudanar da gasar samun izinin shiga gasar ƙarshe ta wasan gudu a kan dusar ƙanƙara cikin ’yanci ta mata ta hanyar tsalle daga dandalin gasar Olympics a lokacin sanyi ta 2022, inda ’yar wasan ƙasar Sin Gu Ailing ta halarci gasar. Bisa labarin da aka samu, an ce, tun daga shekarar 2019, Gu Ailing ta fara shiga gasa a ...
Bisa labarin da shafin Internet na Tianshan na ƙasar Sin ya bayar, an ce, a yammacin shekaranjiya 5 ga watan Fabarairu, Dinigeer Yilamujiang da abokiyar wasanninta a ƙungiyar ƙasar Sin Bayani Jialin suka fara wasannin gudu a kan dusar ƙanƙara na ƙetaren daji na gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing. Haka kuma, wannan shi ne karo na farko da aka samu ’yan wasan daga birnin Altay da...
A ranar 18 ga watan Janairu,an kaddamar da bikin tura matasa masu aikin sa kai na BFSU zuwa gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da gasar wasannin Olympics ta nakasassu. Haka kuma, wannan biki ya kasance bikin fara ba da hidimomi da harsunan daban daban na Beijing a hukunce. Mataimakin shugaban kula da sashen tuntubawar waje na kwamintin shirya wasannin Olympics na Beijing W...
Kwanan baya, an fidda takardar sunayen manyan ayyukan bincike dake shafar kimiyyar zamantakewar al’umma na shekarar 2021. An amince da manyan ayyuka 4 da BFSU ta gabatar, wanda ya dau matsayi na 21 a kasar Sin. A sa’i daya kuma, rukunin kula da asusun nazarin kimiyyar zamantakewar al’ummar Sin ya amince da cewa, BFSU dake karkashin shugabancin farfesa Wang Dinghua, babban sakataren jam’iy...
A ranar 9 ga watan Disamba, an shirya taron tattaunawar masanan gida da waje na kwalejin Confucius na jami’ar BFSU na shekarar 2021. Taken taron shi ne ilmin koyar da Sinanci na kasa da kasa bayan cutar Covid-19, don lalubo bakin zaren warware matsalolin da ake fuskanta wajen koyar da Sinanci, bayan barkewar cutar Covid-19, da tattauna hanyoyin da za a bi wajen tinkarar kalubale, da ...
A ranar 8 ga wata, an shirya bikin karramawar gwarazan da suka yi fice a yayin bikin murnar cika shekaru 80 da kafuwarta. Sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar, Wang Dinghua, da mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma shugaban jami’ar Yang Dan, da mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia ...
A ranar 10 ga watan Nuwamba, aka kaddamar da bikin horar da masu aikin sa kai na wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing na shekarar 2022 na jami’ar BFSU. Mataimakiyar shugabar dake kula da aikin sa kai na kwamintin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing Madam Wang Lina da mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis ta BFSU Su Dapeng sun halarci bikin. Wakilan rukunin kula...