A ranar 31 ga watan Maris, shugabar jami’ar Queensland ta Australiya Deborah Terry ta shugabanci tawaga don ziyartar BFSU. Shugaban BFSU kuma zaunannen kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya gana da shi, inda suka daddale yarjejeniyar fahimtar juna ta haɗin gwiwa a tsakanin jami’o’i biyu
A ranar 23 ga watan Maris, shugaban jami’ar Belarusian Anderi Karol ya shugabanci tawaga don ziyartar BFSU. Shugaban BFSU kuma zaunannen kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Yang Dan ya gana da shi, inda suka daddale yarjejeniyar musayar ɗalibai a tsakaninsu
A ranar 20 ga watan Maris, an ƙaddamar da bikin murnar ranar Faransanci a faɗar ofishin jakadancin Faransa da ke ƙasar Sin. Ma’aikatar ilmi ta ƙasar Faransa ta karrama shugabar kwalejin nazarin harshe da al’adun Faransancin BFSU Dai Dongmei lambar yabo ta nazari, don jinjina ƙoƙarin da ta yi wajen koyar da harshe da yawaita al’adun ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci. Jakadan...
A ranar 20 ga watan Maris, jakadan ƙasar Kazakhstan a ƙasar Sin Shakhrat Nuryshev ya ziyarci BFSU, inda ya halarci bikin buɗe gasar harshen Kazakh karo na farko tsakanin ɗalibai masu koyon harsunan waje na ƙasar Sin. Sakataren kwamitin jami’iyyar kwaminisancin jami’ar Wang Dinghua ya gana da shi, inda suka tattauna batun fara ɗarasin tafinta da bayar da kyautar kuɗin karatu
A ranar 20 ga watan Maris, shugaban Western Sydney na Australiya Barney Glover ya shugabanci tawaga don ziyartar BFSU.Sakataren kwamitin jami’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gana da su, inda bangarorin biyu suka yi shawarwari game da mu’amalar ɗalibai da ziyarar malamai da horar da ɗalibai da raya digiri na biyu tsakaninsu
A ranar 18 ga watan Maris, an gudanar da taron ƙara-wa-juna gani game da raya ma’adanar bayanai wajen nazarin ƙasashe duniya da shiyya-shiyya na ƙasar Sin, inda ƙawacen gamayyar nazarin shiyya-shiyya da ƙasashen duniyar Sin ya shiya wannan taro a BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin BFSU Yang Dan ya halarci taron.A yayin taron, ƙwararru da mas...
A ranar 1 ga watan Maris, mataimakin sashen kula da tuntuɓawar waje na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jikin Asiya Xu Jianfeng ya ziyarci BFSU, inda zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’a kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia Dezhong ya gana da shi, inda suka yi musanyar ra’ayi game da kafa hukumar ba da hidimomin fasara da tafinta ta harsuna da yawa a lokacin wasan...
A ranar 24 ga watan Febrairu, a yayin taron odar littattafan Beijing karo na 35 da aka shirya a birnin Beijing, an shirya taron manema labaru game da sabbin sakamakon fasarar shahararrun adabin ƙasashen Sin da Laos a cibiyar baje-kolin kayayyakin duniya na Sin.An fidda sakamakon fasara jere na farko na ayyukan fassara da Farfesa Lu Yunliang da mataimakiyar farfesa Li Xiaoyuan da malama Lu Hu...
Daga ranar 13 zuwa ranar 14 ga watan Febrairu, an gudanar da taron ilmin raya kimiyya na duniya. Bisa goron gayyata da aka yi, an ce, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan ya halarci taron. Shugaban kwalejin nazarin raya ilmi a kan Intanet kuma mataimakin shugaban kula da dakunan nazarin harsunan duniya da na AI Tang Jinlai ya halarci tar...