Babban Shafi > Labaru > 正文

Jakadan Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa ya ziyarci BFSU

Updated: 2023-05-09

A ranar 4 ga watan Mayu, jakadan ƙasar Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa H.E. Ali Obaid Al Dhaheri ya ziyarci BFSU, kuma babban sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gana da shi.

Ɓangarorin biyu sun yi mu’amala game da ƙara haɗin gwiwa a wajen mu’amalar ɗalibai da ziyarar malamai, da horar da ɗalibai da mu’amalar ilmi a tsakaninsu. Bayan ganawa, Dhaheri ya yi mu’amala da malamai da ɗaliban kwalejin nazarin Arabiyya na BFSU.