Babban Shafi > Labaru > 正文

Mataimakin shugban BFSU ya ziyarci Czech da Italiya

Updated: 2023-05-09

Daga ranar 16 zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia Wenjian ya ziyarci ƙasashen Czech da Italiya, inda ya ziyarci jami’ar Palacký don tattauna haɗin gwiwa wajen kafa kwalejin Confucius, kuma ya ziyarci kwalejin nazarin kasuwancin Moravian don tattauna haɗin gwiwa a tsakaninsu. Haka kuma, ya ziyarci kwalejojin Confucius da ke jami’ar Rome da jami’ar Convitto nazionale Vittorio Emanuele II da halartar ranar Sinanci ta duniya, da tattauna halin da ake ciki game da horar da ɗaliban Italiya a ƙasar Sin a lokacin hutu na zafi. Haka kuma, ya ziyarci jami’ar Istituto Universitario Orientale di NAPOLI don yalwata haƙiƙanin haɗin gwiwa a tsakanin jami’o’i biyu da lalubo sabon alkiblar haɗin gwiwa. Haka kuma, shugaban Jia ya ziyarci ofisoshin jakadancin Sin da ke ƙasashen Czech da Italiya, da mu’amala da jami’ai a wurin, kuma ya gana da abokan karatu da ɗaliban ƙasashen waje da ke ƙasar Italiya.