A ranar 20 ga watan Maris, an ƙaddamar da bikin murnar ranar Faransanci a faɗar ofishin jakadancin Faransa da ke ƙasar Sin. Ma’aikatar ilmi ta ƙasar Faransa ta karrama shugabar kwalejin nazarin harshe da al’adun Faransancin BFSU Dai Dongmei lambar yabo ta nazari, don jinjina ƙoƙarin da ta yi wajen koyar da harshe da yawaita al’adun ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci. Jakadan...
A ranar 20 ga watan Maris, jakadan ƙasar Kazakhstan a ƙasar Sin Shakhrat Nuryshev ya ziyarci BFSU, inda ya halarci bikin buɗe gasar harshen Kazakh karo na farko tsakanin ɗalibai masu koyon harsunan waje na ƙasar Sin. Sakataren kwamitin jami’iyyar kwaminisancin jami’ar Wang Dinghua ya gana da shi, inda suka tattauna batun fara ɗarasin tafinta da bayar da kyautar kuɗin karatu
A ranar 20 ga watan Maris, shugaban Western Sydney na Australiya Barney Glover ya shugabanci tawaga don ziyartar BFSU.Sakataren kwamitin jami’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gana da su, inda bangarorin biyu suka yi shawarwari game da mu’amalar ɗalibai da ziyarar malamai da horar da ɗalibai da raya digiri na biyu tsakaninsu
A ranar 18 ga watan Maris, an gudanar da taron ƙara-wa-juna gani game da raya ma’adanar bayanai wajen nazarin ƙasashe duniya da shiyya-shiyya na ƙasar Sin, inda ƙawacen gamayyar nazarin shiyya-shiyya da ƙasashen duniyar Sin ya shiya wannan taro a BFSU. Shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin BFSU Yang Dan ya halarci taron.A yayin taron, ƙwararru da mas...
A ranar 1 ga watan Maris, mataimakin sashen kula da tuntuɓawar waje na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jikin Asiya Xu Jianfeng ya ziyarci BFSU, inda zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’a kuma mataimakin shugaban jami’ar Jia Dezhong ya gana da shi, inda suka yi musanyar ra’ayi game da kafa hukumar ba da hidimomin fasara da tafinta ta harsuna da yawa a lokacin wasan...
A ranar 24 ga watan Febrairu, a yayin taron odar littattafan Beijing karo na 35 da aka shirya a birnin Beijing, an shirya taron manema labaru game da sabbin sakamakon fasarar shahararrun adabin ƙasashen Sin da Laos a cibiyar baje-kolin kayayyakin duniya na Sin.An fidda sakamakon fasara jere na farko na ayyukan fassara da Farfesa Lu Yunliang da mataimakiyar farfesa Li Xiaoyuan da malama Lu Hu...
Daga ranar 13 zuwa ranar 14 ga watan Febrairu, an gudanar da taron ilmin raya kimiyya na duniya. Bisa goron gayyata da aka yi, an ce, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Yang Dan ya halarci taron. Shugaban kwalejin nazarin raya ilmi a kan Intanet kuma mataimakin shugaban kula da dakunan nazarin harsunan duniya da na AI Tang Jinlai ya halarci tar...
A ranar 12 ga watan Janairu, kwalejin kula da tantance nazarin kimiyyar zamantakewa da al’adun ƙasar Sin ta bayar da rahoto game da tantance mujallolin nazarin kimiyyar zamantakewa da al’adu na ƙasar na AMI na shekarar 2022, inda aka bayar da sakamakon da suka samu. Mujallolin BFSU sun yi fice a cikin wannan aikin tantance na wannan karo, mujalla ɗaya ta zama fitacciyar mujalla, yayin da...
Bisa goron gayyata da shugaban ƙasar Sin Xi jinping ya yi, an ce, daga ranar 5 zuwa ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2023, shugaban ƙasar Turkmenistan Serdar Berdimuhamedov ya kai ziyarar aiki a ƙasar Sin. BFSU ta daddale takardar fahimtar juna da jami’ar Magtymguly ta Turkmenistan, wadda ta kasance cikin sakamakon da aka samu a yayin ziyarar shugaban Turkmenistan a ƙasar Sin.A ranar 6...