
A ranar 6 ga watan Maris, an shirya liyafa don taya murnar ranar mace ta duniya a birnin Beijing. Mambar majalisar gudanarwa kuma shugabar kwamitin ƙungiyar matan Sin Shen Yiqin ta halarci bikin. Sassan da abin ya shafa, da wakilai da mambobin matan da suke halartar tarurruka biyu na NPC da CPPCC, da ragowar mata ta kabilu daban daban, da matan yankin Hongkong da na Macau na ƙasar Sin, da jami’an diflomasiyyar ƙasashen waje da na hukumomin ƙasa da ƙasa a ƙasar Sin kimanin 1000 sun halarci liyafar. Wakilan malaman BFSU 11 su ma sun halarci liyafar.