Babban Shafi > Labaru > 正文

BFSU ta fara tsara shirye-shiryen ayyukan sabon zangon karatu na shekarar 2026

Updated: 2026-03-13

A ranar 28 ga watan Fabrairu, BFSU ta gudanar da taro, inda aka jibgen ayyukan da za a ɗauka a sabon zangon karatu na shekarar 2026. Shugabannin BFSU sun halarci taron. A yayin taron, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Li Hai da mataimakin sakatare kuma shugaban BFSU Jia Wenjian sun tsara matakan da za a ɗauka a sabon zangon karatu.

Game da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, Li Hai ya ce, dole ne a mai da hankali game da raya harsuna, da al’adu, da daidaita lamuran duniya, don ƙara sa ƙaimi ga jami’ar da ta buɗe ƙofa ga ƙasashen waje, da haɓaka mu’amala da ƙasashen duniya, da raya haɗin gwiwa da sanannun jami’o’in duniya, don ɗaukaka kwarjinin jami’ar, da raya kwalejojin Confucius ta gadar Sinanci, ta hakan za a yada al’adun Sin da haɓaka jami’ar. Shugaban Jia ya ce, dole ne a nace kan haɗin gwiwar ƙasashen duniya, da tabbatar da haɗin gwiwa da jami’ar SOAS, da raya sabon salon raya jami’ar, da kyautata dandalin kwalejin Confucius da sansanin ɗaukar ƙwararru, da hagen nesa don tsara shirye-shirye wajen ba da hidimomi ga raya manyan tsare-tsaren ƙasar, da ɗaukaka kwarjinin jami’ar.