Babban Shafi > Labaru > 正文

Sarauniyar Spain ta ziyarci BFSU

Updated: 2025-11-15

A ranar 13 ga watan Nuwanba, sarauniyar ƙasar Spain Letzia ta ziyarci BFSU. Mataimakin ministan ilmin ƙasar Sin Ren Youqun da direktan kula da harkokin haɗin gwiwa da mu’amala Yang Dan, sakataren kwamitin kula da harkokin kwaminisancin Sin Wang Dinghua, da shugaban BFSU Jia Wenjian, da mataimakinsa Zhao Gang sun halarci taron. Malamai da ɗalibai masu koyon harshen Spain na kwalejin harshen Spain da Portugal, da kwalejin koyon ilmin alaƙar ƙasa da ƙasa, da kwalejin ilmi 300 sun halarci taron.

A yayin bikin, letzia da Ren Youqun, da Yang Dan, da Wang Dinghua, da Jia Wenjian sun ganewa idanunsu bikin miƙa bikin tunawa da jinjina malaman harshen Spain da suka zo ƙasar Sin wajen koyar da harshen Spain a cikin shekaru 50 na ƙarni na 20.

Shugaban kwalejin harsunan Spain da Portugal na BFSU Chang Fuliang ya gabatar da yanayin da ake ciki wajen koyar da harshen Spain da BFSU, ɗaliba mai koyon harshen Spain Ma Keying da ɗalibin ƙasar Spain Alberto sun yi shawarwari da harshen Spain da Sinanci, don sanya matasan ƙasashen Sin da Spain su samu fahimtar juna.

Sarauiyar Letzia tana sha’awar aikin koyar da harshen Spain da mu’amala a tsakanin ƙasashen Sin da Spain, kuma sun yi mu’mala da malamai da ɗalibai a wurin.