
A ranar 16 ga watan Oktoba, an yi shawarwari don gudanar da shawarar makomar da jami’ar M.D.D., da ofisoshin M.D.D.dake ƙasar Sin, da jami’ar BFSU, da jami’ar Cape Town sun shirya tare.
Mataimakin direktan dake kula da harkokin ƙasa da ƙasa na ma’aikatar kula da harkokin ilmin Sin Li Hai, da mataimakin sakataren dake kula da harkokin siyasa na M.D.D. Guy Ryder, direktan dake kula da aiwatar da shawarar makomar ofishin sakataren M.D.D. Themba Kaula, kuma jami’in M.D.D. dake ƙasar Sin Siddharth Chatterjee, da sakataren BFSU Wang Dinghua sun halarci bikin,
Taken shawarwari shi ne “Aiwatar da yarjejeniyar makoma, don daidaita batutuwan duniya cikin armashi”. Wakilan jami’o’in ƙasashen duniya, da jami’an M.D.D., da na ma’aikatar kula da harkokin ilmi, da ma’aikatar harkokin waje sun halarci taron.