
A ranar 24 ga watan Oktoba, an gudanar da taron tattaunawa karo na biyar na shugannin ƙawacen jami’o’in harsunan wajen duniya a birnin Hangzhou.
Shugaban kwamitin kula da harkokin mu’amalar ilmi a ƙasashen duiya na ƙasar Sin kuma mataimakin ministan ilmin Sin Liu Liming da shugaban ƙawacen jami’o’in harsunan waje na GAFSU kuma shugaban BFSU Jia Wenjian, da sakatare kuma shugaban kwalejin nazarin harsunan waje na Zhejang Zhang Huanzhou, da sauran shugabannin ƙawacen GAFSU sun halarci taron.
Taken taron shi ne “fuskantar makoma, da raya kimiyya, samun bunƙasuwa”, masana da ƙwararru 170 daga jami’o’i ko hukumomi sama da 60 na ƙasashe 27 sun halarci taron. A yayin taro, an fitar da shawarar samun bunƙasuwar ƙirƙiro da sabbin abubuwa da nazari da koyar da harsuna ta hanyar kimiyya.