
A ranar 15 ga watan Oktoba, mataimakiyar shugaban ƙasar Bulgariya Iliana Iotova ta ziyarci BFSU, inda shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya gana da ita.
Shugaban Jia ya gabatar da yanayin da ake ciki game da mu’amala da ƙasashen waje, da horar da ƙwararru, da haɓaka fannonin karatu da yawa. Ya bayyana cewa, BFSU ta dora muhimmanci sosai game da fannin karatu na harshen Bulgariya da bincikensa, yana fata gwamnatin Bulgariya da ofishin jakadancin Bulgarya da ke ƙasar Sin za su ci gaba da nuna goyon baya da ba da taimako game da wannan fanni. BFSU tana fata za ta yi amfani da wannan harshe don yalwata mu’amala a tsakanin matasa masana na ƙasashen biyu, gami da bayar da babbar gudummawa ga aikin sada zumunta a tsakaninsu. Ta jaddada muhimmancin raya fannonin bincike game da al’adu da kuma mutane, tana sa rai za a ƙara mu’amala tsakanin masana da ɗalibai, kuma ta bayyana cewa, gwamnatin Bulgariya tana fata haɗin gwiwa da BFSU don sada zumunta tsakanin jama’ar ƙasashen biyu ta haɗin gwiwa a fannin ilmi.
Bayan ganawa, Iliana Iotova ta yi jawabi ga malamai da ɗaliban BFSU, inda suka yi musanyar ra’ayoyi a tsakaninsu. A yayin bikin, Iliana Iotova ta ba da lambar yabo ta Bulgariya ga Ma Xipu, manazarci a cibiyar nazarin Bulgariya, don yaba babbar gudummawa da ya bayar wajen nazarn tarihi da al’adun Bulgariya.