Babban Shafi > Labaru > 正文

Shugaban BFSU ya halarci bikin ƙaddamar da cibiyar horar da ɗalibai masu neman digiri na uku na ƙasar Sin da ƙungiyar ƙasashen SCO

Updated: 2025-09-16

Daga ranar 5 zuwa ranar 6 ga watan Satumba, shugaban BFSU kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Jia Wenjian ya halarci bikin ƙaddamar da cibiyar horar da ɗalibai masu neman digiri na uku na ƙasar Sin da ƙungiyar haɗin gwiwa kan ƙasashen Shanghai watau SCO. Mataimakin ministan ilmin Sin Wu Yan, da mataimakin shugaban lardin Heilongjang Sui Hongbo, da shugaban jami’ar BNTU ta Belarus Sergey Haritonchik sun halarci bikin. A yayin bikin, a madadin sauran wakilai, shugban Jia ya yi jawabi, zaunannen mamban kwamintin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban jami’ar Liu Xinlu ya halarci bikin.