Babban Shafi > Labaru > 正文

An ƙaddamar da bikin fara karatu na shekarar 2025

Updated: 2025-09-16

A ranar 1 ga watan Satumban shekarar 2025, an ƙaddamar da bikin fara karatu na shekarar 2025. Sabbin ɗalibai 3917 da suka fito daga ƙasashe 90 da sassan daban daban na Sin sun shiga cikin jami’ar.

Sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua da mataimakinsa kuma shugaban BFSU Jia Wenjian, da mataimakin sakataren kwamitin Jia Dezhong da Su Dapeng, da zaunannen mamban kwamitin kuma mataimakin shugaban jami’ar Ding Hao da Zhao Gang, da jakadan Georgia a ƙasar Sin Paata Kalandadze, da abokin karatu na kwalejin nazarin kasuwancin jami’ar BFSU kuma mai tsara dandanlin World Without Borders Wang Yuhao ya halarci bikin.

Shugaban Jia ya yi maraba da sabbin ɗalibai, inda ya gabatar da fatawarsa game da sabbin ɗalibai.

A nasu bangare, jakadan Kalandadze da wakilan abokin karatu, da malamai, da ɗalibai masu neman digiri na farko da na digirgiri, da ɗaliban ƙasashen waje sun yi jawabi ɗaya bayan ɗaya.

Sakataren Wang ya miƙa katin jami’a ga ɗalibai.

Daga bisani kuma, wakilan sabbin ɗalibai sun miƙa furanni ga wakilan malamai, kuma sun yi rantsuwar shiga cikin jami’ar.