
A ranar 29 ga watan Agusta, shugaban SOAS Adam Habib ya shugabanci tawaga don kai ziyara a jami’ar BFSU. Sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar Wang Dinghua da mataimakin sakataren kwamitin kuma shugaban BFSU Jia Wenjian ya gana da shi, inda ɓangarorin biyu suka yi bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin BFSU da SOAS.
A wannan rana, shugaban Jia ya raka tawagar Habib don kai ziyara a ɗakin nune-nunen kayayyakin tarihin BFSU da bikin da aka shirya wa sabbin ɗalibai don jin daɗin karatu a jami’ar. Sannan kuma, Habib ya yi jawabi mai take, “Ina muke? Rawar da Afirka ta Kudu da nahiyar Afirka suke takawa a duniya.”