Babban Shafi > Labaru > 正文

Sakatare Wang Dinghua ya ziyarci Iceland da Denmark da Sweden

Updated: 2025-09-02

Daga ranar 21 zuwa ranar 29 ga watan Agusta, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya shugabanci tawaga don kai ziyara a ƙasashen Iceland da Denmark da Sweden, inda suka ziyarci jami’ar Iceland da ta Akureyri, da jami’ar Aarhus da ta Copenhagen ta Denmark, da jami’ar Lund da kwamitin mu’amalar ƙasashen waje na Sweden, sannan kuma sun ziyarci ofishin jakdancin Sin a ƙasashen Iceland da Denmark da Sweden, kuma sun yi bincike a kwalejin confucius na Beijiguang a jami’ar Iceland, da sashen Stockholm na bankin Sin, da cibiyar bincike a Turai ta kamfanin samar da wutar lantarki da iska ta Shanghai, kana an shirya taron tattaunawa da bincike a wasu kamfanoni, kuma sun je ganin ɗalibai masu neman digiri na farko na BFSU a Iceland, da shirya taron tattaunawa da ɗaliban da suka taɓa halartar bikin ƙara sanin Sin, sannan sun gai da abokan karatu da suke aiki a Denmark da Sweden.