Babban Shafi > Labaru > 正文

An fara aikin koyarwa na ƙara sanin ƙasar Sin na 2025

Updated: 2025-08-16

A ranar 31 ga watan Yuli, an fara sansanin koyar da Sinanci na ƙara sanin ƙasar Sin na shekarar 2025. Mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Jia Dezhong da mataimakin direktan cibiyar haɗin gwiwa kan mu’amala game da harsunan gida da waje na ma’aikatar ilmin ƙasar Sin Liu Jianqing sun halarci bikin buɗe taro. Malamai da ɗalibai 154 da suka fito daga ƙasashen Czech, da Bulgariya, da Poland, da Austriya, da Koriya ta Kudu, da Malaysiya, da Spaniya, da Italiya da sauran ƙasashe 15.

Cibiyar kula da haɗin gwiwa kan harsunan gida da waje ta ma’aikatar harkokin ilmin Sin da jami’ar BFSU sun gudanar da aikin koyar da Sinanci na ƙara sanin ƙasar Sin. A matsayin wani aikin koyar da Sinanci na duniya da aka koyar wa ɗaliban ƙasashen waje, an sa burin ƙara sanin fahimtar ƙasashen duniya da mu’amala tsakanin ƙasashen waje, da dukufa ka’in da na’in wajen samar da damar koyon Sinanci mai kyau ga ɗaliban ƙasashe daban daban, kuma za a ƙara sanin al’adun Sin da fahimtar ƙasar Sin a zamanin yau ta koyar da harshe da fahimtar al’adu da kai ziyara.