
A ranar 16 ga watan Afrilu, jakadan ƙasar Sweden da ke ƙasar Sin Per Augustsson ya ziyarci BFSU, inda sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya gana da shi. Ɓangarorin biyu sun tattauna game da haɗin gwiwar bincike da ƙarfafa mu’amalar malamai da ɗalibai a tsakaninsu. Kafin tattaunawa, Augustsson ya ziyarci kwalejin nazarin harsuna da al’adun ƙasashen Turai, inda ya yi mu’amala da ɗalibai da malaman harshen Sweden.