
A ranar 22 ga watan Maris, an ƙaddamar da taron tattaunawa karo na 9 game da gyare-gyare kan ilmin harsunan waje da samun bunƙasuwa na jami’o’in ƙasar Sin. A yayin taron tattaunawa, an ƙaddamar da dandalin ba da hidimomin harsunan duniya na BFSU. Bisa ƙa’idar samun bunƙasuwa tare, an kafa dandalin ba da hidimomin harsunan waje, da dandalin raya harkokin ilmin ƙasashen waje, da dandalin nazarin harsunan waje da raya su.