Babban Shafi > Labaru > 正文

Sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU ya ziyarci ƙasashen Austriya da Swiss da Portugal

Updated: 2025-04-02

Daga ranar 20 zuwa ranar 29 ga watan Maris, sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua ya ziyarci ƙasashen Austriya, da Swiss da Portugal, inda ya ziyarci cibiyar nazarin Jelinek ta Austriya, da jami’ar Vienna, da kwalejin Confucius na jami’ar Vienna, da kwalejin nazarin alaƙar ƙasa da ƙasa da samun bunkasuwa na Swiss, da jami’o’in Porto, da Coimbra, da ULisboa na ƙasar Portugal, da ofisoshin M.D.D. dake birane Vienna da Geneva, da ƙungiyar kwadago ta ƙasa da ƙasa, da ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross, da ƙungiyar kare hakkin ilmin ƙasa da ƙasa, da ƙawacen Telecom na ƙasa da ƙasa, da taron tattaunawar tattalin arzikin duniya, da asusun Tianlin. Kana, sun ziyarci ofishin jakadancin Sin dake ƙasar Austriya, da ofishin M.D.D. dake birnin Vienna, da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da ofishin jakadancin Sin da ke ƙasar Portugal. Ban da wannan kuma, an shirya taron ƙara-wa-juna-sani game da abokan karatu na ƙasashen duniya dake ƙasar Swiss, kuma sun ziyarci sashen kamfanin CCCC dake ƙasar Portugal, kuma an buɗe sansanin gwajin aikin ɗaliban BFSU a ƙasar Portugal.