
A ranar 20 ga watan Satumba, shugaban jami’ar Köln kuma shugaban cibiyar musayar ilmi ta Jamus Joybrato Mukherjee ya ziyarci BFSU, inda ya gana da babban sakataren kwamintin tsakiyar jam’iyyar kwaminisancin jami’ar BFSU Wang Dinghua, inda bangarorin biyu suka yi shawarwari game da haɗin gwiwa a fannin nazari da musayar ɗalibai da malamai a tsakaninsu.