A ranar 15 ga wata, BFSU ta shirya bikin buɗe darasin Tetun a hukunce. Wannan shi ne karo na farko ne da aka koyar da darasin Tetun a Sin. Zaunannen mamban kwamintin tsakiya na jami’ar kwaminisancin jami’ar BFSU kuma mataimakin shugaban BFSU Zhao Gang da ƙaramin jakada a fannin ilmi na ofishin jakadancin Timor-Leste dake ƙasar Sin Rogério Paulo Chaves sun halarci bikin gami da gabatar da jawabi. Bayan bikin, an fara koyar da darasin a hukunce.